Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:8 - Littafi Mai Tsarki

8 “ ‘Al'ummar nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:8
11 Iomraidhean Croise  

Ɗana ka mai da hankali sosai, irin zamana ya zamar maka kyakkyawan misali.


Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace.


Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa, Suna girma, suna kuma ba da 'ya'ya, Sunanka na a cikin bakinsu, amma kana nesa da zuciyarsu.


Sukan zo wurinka su zauna, sai ka ce su mutanena ne, sukan ji abin da ka ce, amma ba za su aikata ba, gama suna nuna ƙauna da baka, amma sun ƙwallafa zuciyarsu a kan ƙazamar riba.


Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, da ya ce,


Sai ya ce musu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Al'umman nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni.


Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!”


domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.


Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.


Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.


Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, Sai ya kame bakinsa daga ɓarna, Ya kuma hana shi maganar yaudara.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan