Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:4
18 Iomraidhean Croise  

“Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.


“Wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa, lalle kashe shi za a yi.


Idan ka zagi iyayenka, za ka mutu kamar fitilar da ta mutu cikin duhu.


Ka kasa kunne ga mahaifinka, gama da ba dominsa ba, da ba ka, sa'ad da mahaifiyarka ta tsufa ka nuna mata godiyarka.


Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.


Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”


Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.


“Dukan wanda ya zagi mahaifinsa, ko mahaifiyarsa za a kashe shi, gama ya zagi mahaifinsa da mahaifiyarsa. Alhakin jininsa yana wuyansa.


Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku?


Amma ku kukan ce, ‘Kowa ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’


Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.”


Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Wato mun soke Shari'a ke nan ta bangaskiyar nan? A'a, ko kusa! Sai tabbatar da ita muka yi.


Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.


“ ‘La'ananne ne wanda ya raina mahaifinsa ko mahaifiyarsa.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’


“ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan