Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:33
9 Iomraidhean Croise  

Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”


Yesu ya kira almajiransa, ya ce, “Ina jin tausayin wannan taro, don yau kwanansu uku ke nan a guna ba su da wani abinci. Ba na kuwa so in sallame su da yunwa haka, kada su kasa a hanya.”


Yesu ya ce musu, “Gurasa nawa suke gare ku?” Suka ce, “Bakwai, da ƙananan kifaye kaɗan.”


Amma ya amsa musu ya ce, “Ku ku ba su abinci mana.” Sai suka ce masa, “Wato mu je mu sayo gurasa ta dinari metan, mu ba su su ci?”


Amma ya ce musu, “Ku ku ba su abinci mana.” Suka ce, “Ai, abin da muke da shi bai fi gurasa biyar da kifi biyu ba, sai dai in za mu je mu sayo wa dukkan jama'an nan abinci ne.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan