Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Har jama'ar suka yi ta al'ajabi da ganin bebaye suna magana, masu dungu sun sami gaɓoɓinsu, guragu na tafiya, makafi kuma suna gani, duk suka ɗaukaka Allah na Isra'ila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:31
23 Iomraidhean Croise  

Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”


A wurin ya gina bagade ya sa masa suna El-Elohe-Isra-el.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Wanda yake yin godiya a sa'ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni, Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”


Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.


Taro masu yawan gaske suka zo wurinsa, suka zazzo da guragu, da masu dungu, da makafi, da bebaye, da kuma waɗansu da yawa, suka ajiye su a gabansa, ya kuwa warkar da su.


In kuwa hannunka ko ƙafarka suna sa ka laifi, to, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai dungu ko da gurguntaka, da a jefa ka madawwamiyar wuta da hannu biyu ko ƙafa biyu.


Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.


Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.


Sun tashi ke nan, sai aka kawo masa wani bebe mai aljan.


Bayan an fitar da aljanin, sai beben ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki, suka ce, “Kai! Ba a taɓa ganin irin wannan a cikin Isra'ila ba.”


Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.


Sai ya tashi nan da nan, ya ɗauki shimfiɗarsa, ya fita a gaban idon kowa, har suka yi mamaki duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin irin haka ba!”


Suka yi mamaki gaba da kima, suka ce, “Kai, ya yi kome da kyau! Har kurma ma ya sa ya ji, bebe kuma ya yi magana.”


In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa.


Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi,


Bawan ya dawo ya ba ubangijinsa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce wa bawansa, ‘Fita maza, ka bi titi-titin birni da kwararo-kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.’


Nan take ya sami gani, ya bi Yesu, yana ɗaukaka Allah. Ganin haka, sai duk jama'a suka yabi Allah.


Sai tsoro ya kama su duka, suka ɗaukaka Allah suna cewa, “Lalle, wani annabi mai girma ya bayyana a cikinmu,” da kuma, “Allah ya kula da jama'arsa.”


Sai suka sāke kiran mutumin nan da yake makaho a dā, suka ce masa, “Ka tsoraci Allah dai! Mu kam, mun san mutumin nan mai zunubi ne.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan