Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Sai Yesu ya amsa mata ya ce, “Kai, uwargida, bangaskiyarki da yawa take! Yă zamar miki yadda kike so.” Nan take 'ya tata ta warke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:28
21 Iomraidhean Croise  

Na fid da zuciya ɗungum. To, in Allah ya kashe ni, sai me? Zan faɗa masa ƙarata.


Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne.


Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa, Yakan ji kukansu, ya cece su.


Ko da ya sa ɓacin rai, Zai ji tausayi kuma, Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.


Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”


Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”


Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki, har ya ce wa mabiyansa, “Gaskiya, ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.


Sai Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka, ya zama maka gwargwadon bangaskiyar da ka yi.” Nan take yaronsa ya warke.


Sai Yesu ya juya, yă gan ta, ya ce, “'Yata, ki yi farin ciki, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take matar ta warke.


Sai ya ce mata, “'Yata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya, ki warke daga cutarki.”


Sai manzanni suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya.”


Sai Yesu ya ce wa matar, “Bangaskiyarki ta cece ki. Ki sauka lafiya.”


Da Yesu ya ji haka, ya yi mamakinsa, ya kuma juya ya ce wa taron da suke biye da shi, “Ina gaya muku, ko a cikin Isra'ila ban taɓa samun bangaskiya mai ƙarfi irin wannan ba.”


Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan