Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:26
10 Iomraidhean Croise  

Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”


Sai ta ce, “I, haka ne, ya Ubangiji, amma ai, karnuka sukan ci suɗin 'ya'ya.”


“Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”


Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.


“Mu da aka haifa Yahudawa, ba al'ummai masu zunubi ba,


Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama'ar Isra'ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya.


Ku yi hankali da karnukan nan! Ku yi hankali da mugayen ma'aikatan nan! Ku yi hankali da masu yankan jikin nan!


Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan