25 Amma ta zo ta durƙusa a gabansa, ta ce, “Ya Ubangiji, ka taimake ni mana!”
25 Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”
Sa'an nan sai mutumin ya ce, “Ka bar ni in tafi, gama gari na wayewa.” Amma Yakubu ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye. Ya yi kuka, ya roƙi albarka. Ya sadu da Allah a Betel, A can Allah ya yi magana da shi.
Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”
Ya amsa ya ce, “Ai, bai kyautu a bai wa karnuka abincin 'ya'ya ba.”
Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”
Sai ga wani kuturu ya zo gunsa ya yi masa sujada, ya ce, “Ya Ubangiji, in dai ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.”
Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.”
Nan da nan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!”