“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.
Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.
Ina dai gaya muku, Almasihu ya zama bara ga Isra'ila, domin nuna gaskiyar Allah, domin kuma tabbatar da alkawaran nan, da Allah ya yi wa kakannin kakanninmu,