Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:23
8 Iomraidhean Croise  

Da Yusufu ya ga 'yan'uwansa, ya gane da su, amma ya mai da su kamar baƙi, ya yi musu magana da gautsi ya ce, “Daga ina kuka fito?” Suka ce, “Daga ƙasar Kan'ana muka zo sayen abinci.”


Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni, Ka ji kukana! In kuwa ba ka amsa mini ba, Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira.


Ko da yake ina kira, ina kukan neman taimako, Ya yi watsi da addu'ata.


Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”


Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.”


Ya amsa ya ce, “Ni wurin ɓatattun tumakin jama'ar Isra'ila kaɗai aka aiko ni.”


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan