Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Ga wata Bakan'aniya mutuniyar ƙasar, ta zo, ta ɗaga murya ta ce, “Ya Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayina. Wani aljani ya bugi 'yata, ba yadda take.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:22
19 Iomraidhean Croise  

Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!


Mutanen Taya za su kawo miki kyautai, Attajirai za su zo su sami farin jini a gare ki.


Ka ji tausayina, gama na gaji tiƙis, Ka wartsarkar da ni, gama na tafke sarai.


ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda suke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji.


Littafin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda, zuriyar Ibrahim ke nan.


Amma bai ce da ita kanzil ba. Sai almajiransa suka zo suka roƙe shi, suka ce, “Sallame ta mana, tana binmu tana cika mana kunne da kuka.”


“Ya Ubangiji, ka ji tausayin ɗana, yana farfaɗiya, yana shan wuya ƙwarai, sau da yawa yakan faɗa wuta da kuma ruwa.


Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.


Da Yesu ya yi gaba daga nan, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna ɗaga murya suna cewa, “Ya Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu.”


Sai suka ɗaga murya suka ce, “Ya Maigida Yesu, ka ji tausayinmu,”


Mai karɓar haraji kuwa yana tsaye daga can nesa, bai yarda ya ɗaga kai sama ba, sai dai yana bugun ƙirjinsa, yana cewa, ‘Ya Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi!’


Waɗanda kuma baƙaƙen aljannu suke wahalshe su, aka warkar da su.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan