Ubangiji kuwa ya ba da su a hannun Isra'ilawa, suka kuwa ɗibge su, suka runtume su, har zuwa Sidon Babba, da Misrefot-mayim, har zuwa gabashin kwarin Mizfa. Suka karkashe su ƙaƙaf.
da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.