Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Don daga zuci mugayen tunani suke fitowa, kamar su kisankai, da zina, da fasikanci, da sata, da shaidar zur, da yanke.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:19
24 Iomraidhean Croise  

Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.


Sa'ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la'anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā.


Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci, Amma ina ƙaunar dokarka.


Halin yara ne su yi wauta da waɗansu abubuwa na rashin kula, amma tsumagiya za ta koya musu abin da ya fi kyau.


Kowace irin dabarar da wawa yake tunani a kanta zunubi ne. Jama'a suna ƙin mutum mai rainako.


Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.


A kowane lokaci suna shirya mugunta a kangararren hankalinsu, suna kuta tashin hankali ko'ina.


Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.


Kukan sheƙa a guje don ku aikata mugunta, kuna gaggawar zub da jinin marasa laifi. Tunaninku tunanin mugunta ne, lalatarwa da hallakarwa suna a manyan karaukunku.


“Zuciya ta fi kome rikici, Cuta gare ta matuƙa, Wa zai san kanta?


Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, Domin a cece ki, Har yaushe mugayen tunaninki za su yi ta zama a cikinki?


Bal'amu ya ce mata, “Domin kin shashantar da ni, da a ce ina da takobi a hannuna, da na kashe ki.”


Waɗannan suke ƙazantar da mutum. Amma a ci da hannu marar wanki ba ya ƙazantar da mutum.”


Amma ni ina gaya muku, kowa ya dubi mace duban sha'awa, ya riga ya yi zinar zuci ke nan da ita.


Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?


Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.


Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan