Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:18
14 Iomraidhean Croise  

Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi, Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.


Adalai sun san irin maganar da ta cancanta su faɗa, amma mugaye, kullum sukan faɗi maganar da za ta cutar.


Sa'ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha'awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.


Mutanen kirki sukan yi tunani kafin su ba da amsa. Mugaye suna da saurin ba da amsa, amma takan jawo wahala.


Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.


Sakarkari, wato mugaye sukan yi ta baza jita-jita.


Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.


Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”


Ashe, ba ku gane ba, kome ya shiga mutum ta baka, cikinsa ya shiga, ta haka kuma zai fice?


Ya kuma ce, “Abin da yake fita daga cikin mutum yake ƙazanta shi.


Sai ya ce masa ‘Kai mugun bawa! Zan yi maka shari'a bisa ga abin da ka faɗa da bakinka. Ashe, ka sani ni mutum ne mai tsanani, mai son banza, ina kuma girbar abin da ba ni na shuka ba?


Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan