Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne. In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:14
19 Iomraidhean Croise  

Masarawa su ba Allah ba ne, mutane ne kurum! Dawakansu ba su wuce ikon ɗan adam ba! Sa'ad da Ubangiji zai matsa, ƙaƙƙarfar al'umma za ta marmashe, al'ummar da aka yi wa taimako kuma za ta fāɗi. Dukansu za su hallaka.


Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta, Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?


Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi!


Su waɗanda suke bi da jama'an nan, sun bashe su, sun ruɗar da su ɗungum.


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Sun ji kunya sa'ad da suka aikata abubuwan banƙyama? Ba su ji kunya ba ko kaɗan. Ko gezau ba su yi ba, Don haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a hamɓarar da su. Ni Ubangiji na faɗa.”


Ko sun ji kunya Sa'ad da suka aikata ayyuka masu banƙyama? A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan, Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba. Domin haka za su faɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a ci su da yaƙi. Ni Ubangiji na faɗa.


Mutanen Ifraimu sun haɗa kai da gumaka, Sai a rabu da su.


“Amma ku firistoci kun kauce daga hanya. Kun sa mutane da yawa su karkace saboda koyarwarku. Kun keta alkawarin da na yi da ku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Ya kuma ba su wani misali ya ce, “Makaho yana iya yi wa makaho jagora? Ashe, dukansu biyu ba sai su fāɗa a rami ba?


Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”


da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.


Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.


Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan