Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 15:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da yake Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 15:13
11 Iomraidhean Croise  

Za su zama kamar itatuwan da aka daddasa a Haikalin Ubangiji, Suna ta yabanya a Haikalin Allahnmu.


Dukan mutanenki za su yi abin da yake daidai, Za su kuwa mallaki ƙasar har abada. Ni na dasa su, ni na yi su Domin su bayyana girmana ga duka.


Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.


Sai almajiran suka zo suka ce masa, “Ka san Farisiyawa sun ji haushi da suka ji maganan nan?”


“Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi.


Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.


Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.


gama mu abokan aiki ne na Allah, ku kuwa gona ce ta Allah, ginin Allah kuma.


Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan