Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 14:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Amma da uwa tasa ta zuga ta, sai ta ce, “A ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi yanzu yanzu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 14:8
17 Iomraidhean Croise  

Ashe, ba ka ji ba? Na kasa annabawan Ubangiji biyu, na ɓoye su a kogo hamsin hamsin, sa'ad da Yezebel ta kashe annabawan Ubangiji, na ciyar da su, na kuma shayar da su.


A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.


Sai Yezebel ta aike a wurin Iliya ta ce, “Idan gobe war haka, ban kashe ka ba kamar yadda ka karkashe annabawan nan, to, alloli su hukunta ni.”


Sa'ad da Ataliya, uwar Ahaziya, ta ga ɗanta ya rasu, sai ta tashi ta hallaka dukan 'ya'yan sarauta.


Yawan kayayyakin ke nan, kwanonin zinariya guda talatin, da kwanonin azurfa guda dubu (1,000), da wuƙaƙe guda ashirin da tara,


Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai.


Mutane masu kisankai suna ƙin amintaccen mutum, amma adalai za su kiyaye ransa.


aka kuwa kawo kan a cikin akushi, aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa uwa tasa.


har ma ya yi mata rantsuwa zai ba ta duk abin da ta roƙa.


Sai sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwa tasa da kuma baƙinsa, ya yi umarni a ba ta.


Ta fita, ta ce wa uwa tata, “Me zan roƙa?” Uwar ta ce, “Kan Yahaya Maibaftisma.”


Nan da nan sai ta shigo wurin sarki da gaggawa, ta roƙe shi, ta ce, “Ina so yanzu yanzu ka ba ni kan Yahaya Maibaftisma a cikin akushi.”


ya kawo kan a cikin akushi, ya ba yarinyar, yarinyar kuwa to ba uwa tata.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan