Ka faɗa masa, ni Ubangiji, na ce, ‘Ka kashe mutum, kana kuma ƙwace abin da ya mallaka?’ Ka faɗa masa ga abin da na faɗa, ‘A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka.’ ”
Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”