32 Da shigarsu jirgin iska ta kwanta.
32 Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta.
Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”
Na cikin jirgin suka yi masa sujada, suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.”
Sai suka tsorata, matuƙar tsoro, suka ce wa juna, “Wa ke nan kuma, wanda har iska da ruwan teku ma suke yi masa biyayya?”
Sa'an nan ya shiga jirgi wurinsu, iska kuma ta kwanta. Sai mamaki ya kama su ƙwarai,
Sa'an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin. Nan da nan sai ga jirgin a gāɓar da za su.