Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 14:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 14:3
18 Iomraidhean Croise  

To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,


To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,


To, da Yesu ya ji an tsare Yahaya, sai ya tashi zuwa ƙasar Galili.


Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.


Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,


Da 'yar Hirudiya ta shigo ta yi rawa, sai ta gamshi Hirudus da baƙinsa. Sai fa sarki ya ce wa yarinyar, “Roƙe ni kome, sai in ba ki.”


Ya gargaɗe su ya ce, “Ku kula, ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Hirudus.”


Nan take waɗansu da suke a wurin suka ba shi labarin Galilawan da Bilatus ya sa aka kashe, har jininsu ya gauraya da na yankan da suka yi na hadaya.


Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.”


Sai Hirudus da sojansa suka wulakanta shi, suka yi masa ba'a, da suka sa masa tufafi masu ƙawa kuma, suka mai da shi wurin Bilatus.


Da ya ji Yesu a ƙarƙashin mulkin Hirudus yake, sai ya aika da shi wurin Hirudus, don shi ma yana Urushalima a lokacin.


A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,


da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.


A lokacin nan kuwa sarki Hirudus ya fara gwada wa waɗansu 'yan Ikkilisiya tasku,


Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan