Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 14:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Bayan ya sallami taron, ya hau dutse shi kaɗai domin ya yi addu'a. Har magariba ta yi yana can shi kaɗai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 14:23
11 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu'a.”


Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.


Da asussuba ya tashi ya fita, ya tafi wani wuri inda ba kowa, ya yi addu'a a can.


Bayan ya sallame su, sai ya hau dutse domin ya yi addu'a.


To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre,


Amma shi, sai ya riƙa keɓanta a wuraren da ba kowa, yana addu'a.


A kwanakin nan Yesu ya fita ya hau dutse domin yin addu'a. Dare farai yana addu'a ga Allah.


Wata rana yana addu'a shi kaɗai, almajiransa kuwa suka zo wurinsa. Sai ya tambaye su, ya ce, “Wa mutane suke cewa nake?”


Bayan misalin kwana takwas da yin maganan nan, Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, ya hau wani dutse domin yin addu'a.


Mu kuwa sai mu nace da yin addu'a da kuma koyar da Maganar.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan