Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 14:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har suka kwashe ragowar gutsattsarin, cike da kwando goma sha biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 14:20
21 Iomraidhean Croise  

“Na ji gunagunin Isra'ilawa, amma ka faɗa musu cewa, ‘A tsakanin faɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe za ku kuma ƙoshi da abinci. Sa'an nan za ku sani, ni Ubangiji Allahnku ne’ ”


Musa ya kuma ce, “Da yamma Ubangiji zai ba ku nama ku ci, da safe kuwa zai ƙosar da ku da abinci, gama Ubangiji ya riga ya ji irin gunagunin da kuka yi a kansa. Ai, gunagunin ba a kanmu yake ba, wane mu? A kan Ubangiji ne kuka yi.”


Adalai suna da isasshen abinci, amma mugaye fama suke da yunwa ko yaushe.


Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.


Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”


Waɗanda suka ci kuwa misalin maza dubu biyar ne banda mata da yara.


Sai almajiran suka ce masa, “Ina za mu samo gurasa a jeji haka da za ta isa ciyar da ƙasaitaccen taro haka?”


“Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.


Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri, Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.


Duka kuwa suka ci suka ƙoshi, har aka kwashe ragowar gutsattsarin, kwando goma sha biyu.


Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan