Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 14:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 14:19
24 Iomraidhean Croise  

Sai ya ce, “Ku kawo mini su.”


Sa'an nan ya yi umarni dukkansu su zazzauna ƙungiya ƙungiya a ɗanyar ciyawa.


Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.


Ya ɗaga kai sama ya yi ajiyar zuciya, sai ya ce masa, “Iffata!” wato “Buɗu!”


Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.


Sai ya ɗauki gurasa, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba su, ya ce, “Wannan jikina ne da za a bayar dominku. Ku riƙa yin haka, domin tunawa da ni.”


Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.


Maza sun yi wajen dubu biyar. Sai ya ce wa almajiransa, “Ku ce musu su zazzauna ƙungiya ƙungiya, kowace ƙungiya misali hamsin hamsin.”


Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyu, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura su, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a.


Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.


Akwai kuwa waɗansu ƙananan jirage daga Tibariya da suka iso kusa da wurin nan da taron suka ci gurasa bayan Ubangiji ya yi godiya.


Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa'an nan ya gutsuttsura ya fara ci.


Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.


Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba?


To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.


bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura, ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.”


Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.


Da shigarku garin, za ku same shi kafin ya tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu, gama jama'a ba za su ci ba, sai ya je ya sa albarka a sadakar, sa'an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura yanzu, za ku same shi nan da nan.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan