Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.
Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa. Da ya ɗauki gurasan nan bakwai, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiransa su kai wa taron, suka kuwa kakkai musu.