16 Yesu ya ce, “Ba lalle su tafi ba. Ku ku ba su abinci mana.”
16 Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”
Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.
Ka raba abin da yake hannunka ga mutum bakwai ko takwas, gama ba ka san irin masifar da za ta auka wa duniya ba.
Da maraice ya yi, almajiransa suka zo gare shi, suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuwa, rana ta sunkuya. Sai ka sallami taron, su tafi ƙauyuka su saya wa kansu abinci.”
Sai suka ce masa, “Ai, gurasa biyar da kifi biyu kawai muke da su a nan.”
Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”
Har waɗansu ma sun yi zaton Yesu ya ce masa ya yi musu sayayyar idi ne, ko kuwa ya ba gajiyayyu wani abu, don Yahuza ne yake riƙe da jakar kuɗinsu.