Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba'a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba'a, sai Ubangiji ya husata da jama'arsa don abin ya kai intaha.
Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa san shi ne ba, har ma suka yi masa abin da suka ga dama. Haka kuma Ɗan Mutum zai sha wuya a hannunsu.”