A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,
To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.
Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.