Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:8
11 Iomraidhean Croise  

Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,


Wanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, shi ne wanda yake jin Maganar, ya kuma fahimce ta. Hakika shi ne mai yin amfani har ya yi albarka, wani riɓi ɗari, wani sittin, wani kuma talatin.”


Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su.


Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa, su ne kwatancin waɗanda suke jin Maganar, su karɓa, su kuma amfana, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”


Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi yabanya, suka girma, suka yi tsaba, waɗansu riɓi talatin talatin, waɗansu sittin sittin, waɗansu ma har ɗari ɗari.”


Waɗanda aka shuka a ƙasa mai kyau kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, suka riƙe ta kamkam da zuciya ɗaya kyakkyawa, suka jure har suka yi amfani.


Waɗansu kuwa suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka girma, suka yi ƙwaya riɓi ɗari ɗari.” Da ya faɗi haka, sai ya ta da murya ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”


Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina.


Don na sani ba wani abin kirki da ya zaune mini, wato a jikina. Niyyar yin abin da yake daidai kam, ina da ita, sai dai ikon zartarwar ne babu.


kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan