Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:57 - Littafi Mai Tsarki

57 Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

57 Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:57
19 Iomraidhean Croise  

Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.


Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.


Saboda tsananin tsarkina na zama kamar dutse wanda mutane suke tuntuɓe da shi. Na zama kamar tarko wanda zai kama jama'ar mulkokin Yahuza da Isra'ila da mutanen Urushalima.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Bai kuma yi mu'ujizai masu yawa a can ba, saboda rashin bangaskiyarsu.


Ya tashi daga nan ya koma garinsu, almajiransa kuwa suka bi shi.


Sai fa sarki Hirudus ya ji labari, domin sunan Yesu ya riga ya shahara, har waɗansu suka ce, “Yahaya Maibaftisma ne aka tasa daga matattu, shi ya sa mu'ujizan nan suke aiki ta wurinsa.”


Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.


Sai Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu, da cikin 'yan'uwansa, da kuma gidansu.”


Ya ce kuma, “Hakika, ina gaya muku, ba annabin da yake yardajje a garinsu.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu.


Suka ce, “Ashe, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusufu, wanda uwa tasa da ubansa duk mun san su? To, yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko ne daga sama’?”


Yesu kuwa, da yake ya sani a ransa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce musu, “Wato, wannan ne ya zamar muku abin tuntuɓe?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan