Mattiyu 13:55 - Littafi Mai Tsarki55 Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba? Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202055 Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? Faic an caibideil |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.