Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:5
9 Iomraidhean Croise  

Zan ba su zuciya ɗaya, in kuma sa sabon ruhu a cikinsu. Zan kawar musu da zuciya ta dutse, in ba su zuciya mai taushi,


Zan ba ku sabuwar zuciya, in sa sabon ruhu a cikinku. Zan cire zuciya mai tauri daga gare ku, sa'an nan in sa muku zuciya mai taushi.


Dawakai sukan yi sukuwa a duwatsu? Ana huɗan teku da garmar shanu? Duk da haka kuka mai da adalci dafi, Kuka mai da nagarta, mugunta.


Suka taurare zuciyarsu kamar dutse don kada su ji dokoki da maganar da ni Ubangiji Mai Runduna na aiko ta wurin Ruhuna zuwa ga annabawa na dā. Domin haka ni Ubangiji Mai Runduna na aukar musu da hasala mai zafi.


Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.


Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su.


Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.


Haka kuma waɗanda aka shuka a wuri mai duwatsu, su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar sai su karɓa da farin ciki.


Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan kuwa suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan