Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:47 - Littafi Mai Tsarki

47 “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

47 “Har yanzu, mulkin sama yana kama da abin kamun kifin da aka jefa cikin tafki yă kamo kifi iri-iri.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:47
33 Iomraidhean Croise  

Masunta za su tsaya a gāɓar tekun daga En-gedi zuwa En-eglayim. Gāɓar teku za ta zama wurin shanya taruna. Za a sami kifaye iri iri a cikinta kamar kifaye na Bahar Rum.


“Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”


Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”


Da ya cika, aka jawo shi gaci, aka zauna, aka tsince kyawawan kifi, aka zuba a goruna, munanan kuwa aka watsar.


Sai ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”


Yesu ya ce musu, “Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.”


haka ma Yakubu da Yahaya 'ya'yan Zabadi, abokan sabgar Bitrus. Sai Yesu ya ce wa Bitrus, “Kada ka ji tsoro. Nan gaba mutane za ka riƙa kamowa.”


Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.


Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.


Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin 'yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al'ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin 'yan'uwa na ƙarya.


Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai. “ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan