Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:46 - Littafi Mai Tsarki

46 Da ya sami lu'ulu'u ɗaya mai tamanin gaske, sai ya je ya sai da dukan mallaka tasa, ya saye shi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

46 Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:46
15 Iomraidhean Croise  

Ka nema da iyakar ƙoƙarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin ɓoyayyiyar dukiya.


zai kuma sa aminci cikin al'ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama'arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.


“Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”


“Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja.


“Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.


Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.


Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina.


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


wanda shi ne taska, wato maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani.


wato, zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, da lallausan lilin, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da itacen ƙanshi iri iri, da kayan hauren giwa iri iri, da kayan da aka sassaƙa da itace mai tsada, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi,


Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu'ulu'u ne goma sha biyun, kowace ƙofa da lu'ulu'u guda aka yi ta, hanyar birnin kuwa zinariya ce zalla garau kamar ƙarau.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan