Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:43 - Littafi Mai Tsarki

43 Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:43
14 Iomraidhean Croise  

Jama'ar Isra'ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa'an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.


Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.


Duk mai kunnen ji, yă ji.


Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.


Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’


Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”


In da mai kunnen ji, yă ji.”


“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.


Kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka, ni ma nake ba ku iko,


Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.


Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan