Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:38
27 Iomraidhean Croise  

Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


Zuriya masu zuwa za su bauta masa, Mutane za su ambaci Ubangiji ga zuriya mai zuwa.


Ubangiji ya ce, “Nufina ne ya sha wahala, Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara, Saboda haka zai ga zuriyarsa, Zai yi tsawon rai, Ta wurinsa nufina zai cika.


Zan dasa ta a ƙasa domin kaina. Zan kuma yi wa ‘Ba-jinƙai,’ jinƙai, In kuma ce wa ‘Ba-mutanena ba,’ ‘Mutanena!’ Su ma za su ce, ‘Kai ne Allahna!’ ”


Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”


Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A'a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”


'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”


a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.


Lalle hakika, ina gaya muku, in ba an binne ƙwayar alkama ta mutu ba, za ta zauna ita kaɗai. Amma in ta mutu sai ta hayayyafa.


Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.


ya ce, “Kai babban maha'inci, munafiƙi, ɗan Iblis, magabcin adalci duka, ba za ka daina karkata miƙaƙƙun hanyoyin Ubangiji ba?


Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji. “Muryarsu ta gama duniya duka, Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”


Asirin nan kuwa sanar da shi ga dukan al'ummai, ta wurin littattafan annabawa, bisa ga umarnin Allah Madawwami, domin a jawo su, su gaskata, su yi biyayya.


In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.


wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.


Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.


Ku saurara, ya 'yan'uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi matalautan duniyar nan su wadata da bangaskiya, har su sami gado a cikin mulkin nan da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.


Ya ku ƙaunatattuna, a yanzu mu 'ya'yan Allah ne, yadda za mu zama nan gaba kuwa, ba a bayyana ba tukuna, amma mun sani sa'ad da ya bayyana, za mu zama kamarsa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.


Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan