Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Ita ce mafi ƙanƙanta a cikin ƙwayoyi, amma in ta girma, sai ta fi duk sauran ganyaye, har ta zama itace, har ma tsuntsaye su zo su yi sheƙarsu a rassanta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka sa’ad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:32
20 Iomraidhean Croise  

A itatuwan da suke kusa da wurin, Tsuntsaye suke yin sheƙunansu suna ta raira waƙa.


Dukan tsuntsayen sararin sama sun yi sheƙunansu a rassansa, Namomin jeji kuma suka haifi 'ya'yansu ƙarƙashin rassansa. Dukan al'ummai suka zauna ƙarƙashin inuwarsa.


Yana da ganyaye masu kyau Da 'ya'ya jingim don kowa da kowa ya ci. Namomin jeji suka sami inuwa a ƙarƙashinsa, Tsuntsayen sama kuma suka zauna a rassansa. Dukan masu rai a gare shi suka sami abinci.


Gama wane ne ya taɓa raina ranar ƙananan abubuwa? Amma za su yi murna da ganin igiyar awo a hannun Zarubabel. Waɗannan fitilu bakwai su ne alama Ubangiji yana kai da kawowa a duniya.”


Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulkin Allah? Ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?


duk da haka in an shuka ta, sai ta girma ta fi duk sauran ganye, ta yi manyan rassa, har tsuntsaye su iya sauka a inuwarta.”


Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi?


To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin 'yan'uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce,


Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan