Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 “Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:27
17 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.


Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana.


Sai ya ce musu, ‘Wani magabci ne ya yi wannan aiki.’ Bayin suka ce masa, ‘To, kana so mu je mu cire mu tara ta?’


“Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi.


Ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.


In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.


Da yake kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na'am da alherin Allah a banza.


Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da ƙuntata, da masifu,


Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan