Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:25
19 Iomraidhean Croise  

Da tsakar daren sai ta tashi, ta ɗauke ɗana daga wurina, sa'ad da nake barci, ta kai shi gadonta, sa'an nan ta kwantar da mataccen ɗanta a wurina.


Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.


Da shukar ta tashi, ta yi ƙwaya, sai ciyawar ta bayyana.


Sai bayin maigidan suka zo, suka ce masa, ‘Maigida, ashe, ba kyakkyawan iri ka yafa a gonarka ba? To, ta yaya ke nan ta yi ciyawa?’


Amma ya ce, ‘A'a, kada garin cire ciyawar ku tumɓuke har da alkamar ma.


Ku bari su zauna tare har lokacin yanka. A lokacin yanka kuma zan gaya wa masu yankan su fara yanke ciyawar su tara, su ɗaure dami dami a ƙone, alkamar kuwa su taro ta su sa a taskata.’ ”


Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne.


Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.


Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.


Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,


Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame.


Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.


Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.


Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.


Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan