Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Ya kawo musu wani misali kuma, ya ce, “Za a kwatanta Mulkin Sama da mutumin da ya yafa iri mai kyau a gonarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Yesu ya ba su wani misali. “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:24
23 Iomraidhean Croise  

Yana ƙoƙari ya koya mana baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi.”


Saboda haka ne Ubangiji zai koya muku baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi. Sa'an nan kowane ɗaga ƙafar da kuka yi, za ku yi tuntuɓe, za a yi muku rauni, a kama ku a tarko, a kai ku kurkuku.


“Ɗan mutum, ka faɗa wa mutanen Isra'ila ka-cici-ka-cici, da kuma misali.


Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


Sa'ad da mutane suke barci, sai anokin gābansa ya je ya yafa irin wata ciyawa a cikin alkamar, ya tafi abinsa.


Ya kawo musu wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar ƙwayar mastad yake, wadda wani mutum ya je ya shuka a lambunsa.


Ya kuma ba su wani misali, ya ce, “Mulkin Sama kamar yisti yake, wanda wata mace ta ɗauka ta cuɗe da mudu uku na garin alkama, har duk garin ya game da yistin.”


Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.


“Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar taru yake da aka jefa a teku, ya kamo kifi iri iri.


“Saboda haka za a misalta Mulkin Sama da wani sarkin da yake so ya yi ƙididdigar dukiyarsa da yake hannun bayinsa.


“Mulkin Sama kamar wani maigida yake, wanda ya fita da sassafe ya ɗauki ma'aikata don aikin garkarsa ta inabi.


“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.


“Za a kwatanta Mulkin Sama da wani sarki, wanda ya yi wa ɗansa biki.


“Sa'an nan za a kwatanta Mulkin Sama da 'yan mata goma da suka ɗauki fitilunsu suka tafi taryen ango.


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


Sai Yesu ya ce, “Da me Mulkin Allah yake kama? Da me kuma zan kwatanta shi?


Ya sāke cewa, “Da me zan kwatanta Mulkin Allah?


saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,


Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan