Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Amma kuwa ba shi da tushe, rashin ƙarƙo gare shi kuma, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru saboda Maganar, sai ya yi tuntuɓe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:21
47 Iomraidhean Croise  

‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?’ Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini.


Maganarsa mugunta ce cike da ƙarairayi, Ba shi da sauran isasshiyar hikima da zai aikata nagarta.


Iyakar abin da mugaye suke so, shi ne su sami muguntar da za su yi, amma adalai suna tsaye daram.


Mugunta ba ta kawo zaman lafiya, amma adalai sukan tsaya daram.


Ubangiji ya ce, “Me zan yi da ke, ya Ifraimu? Me zan yi da ke, ya Yahuza? Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi, Kamar kuma raɓar da take watsewa da wuri.


Kowa kuma zai ƙi ku saboda sunana. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.


Sai suka yi tuntuɓe sabili da shi. Amma Yesu ya ce musu, “Ai, annabi ba ya rasa girma sai dai a garinsu da kuma a gidansu.”


Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.


Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.


Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’


Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.”


Su kam, ba su da tushe, rashin ƙarƙo gare su, har in wani ƙunci ko tsanani ya faru domin wannan Magana, nan da nan sai su yi tuntuɓe.


Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.


Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami.


In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu.


Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu.


har ma Almasihu yă zauna a zukatanku ta wurin bangaskiyarku, domin ƙauna ta kahu da gindinta sosai a zukatanku,


Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.


Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas.


domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.


Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


“ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan