Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Duk sa’ad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:19
36 Iomraidhean Croise  

In kana so ilimi dole ne ka fara da tsoron Ubangiji. Jahilai ba su san darajar hikima ba, sun kuwa ƙi su koya.


Kashe kuɗi saboda ilimi ba shi da amfanin kome ga wawa, domin ba shi da tunani.


“A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir'auna ke nan, da dukan jama'arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, yā rabu a kan gāba ke nan. To, ta yaya mulkinsa zai ɗore?


Wanda ya faɗa a wuri mai duwatsu kuwa, shi ne wanda da zarar ya ji Maganar Allah, sai ya karɓa da farin ciki.


Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


Abin da duk za ku faɗa ya tsaya a kan ‘I’ ko ‘A'a’ kawai. In dai ya zarce haka, to, daga Mugun ya fito.”


Waɗanda suka fāda a hanya kuwa, su ne kwatancin waɗanda aka shuka Maganar a zuciya tasu. Da zarar sun ji, nan da nan sai Shaiɗan ya zo ya ɗauke Maganar da aka shuka a zuciya tasu.


Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’


ya kuma aike su su yi wa'azin Mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.


Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne, wai shi gaskiya?” Bayan da ya faɗi haka, ya sāke fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba.


Don me ba kwa gane maganata? Don ba kwa iya jimirin jin maganata ne.


Da dai suka ji maganar tashin matattu, sai waɗansu suka yi ba'a, amma waɗansu suka ce, “Game da wannan magana kam, mā sāke jin abin da za ka faɗa.”


Amma tun da yake gardama ce kawai a kan kalmomi, da sunaye, da kuma shari'arku, ai, sai ku ji da ita, ku da kanku. Ni kam, ba ni da niyyar yin shari'a irin waɗannan abubuwa.”


To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.


Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala.


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


don duk a hukunta waɗanda suka ƙi gaskata gaskiya, suke kuma jin daɗin mugunta.


Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.


kada mu zama kamar Kayinu, wanda yake na Mugun, har ma ya kashe ɗan'uwansa. To, don me ya kashe shi? Don ayyukansa mugaye ne, na ɗan'uwansa kuwa na kirki ne.


Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan