Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su gane a zuciyarsu, su kuwa juya, in kuma warkar da su.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:15
25 Iomraidhean Croise  

Waɗannan mutane ba su da ganewa, Amma ni ina murna da dokarka.


Ka kula da mutane masu murguɗa baki suna kaɗa gira a kanka, sun yi tunanin wani mugun abu ke nan.


Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.


“Na ga al'amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta'azantar da su tare da masu makoki.


Sa'an nan ya ce mini, “Ka sa hankalin mutanen nan ya dushe, kunnuwansu su kurunce, idanunsu su makance, har da ba za su iya gani, ko ji, ko fahimta ba. In da za su yi haka mai yiwuwa ne su sāke juyowa gare ni in warkar da su.”


Ubangiji, ka warkar da ni, zan kuwa warke, Ka cece ni, zan kuwa cetu, Gama kai ne abin yabona.


“Zuciya ta fi kome rikici, Cuta gare ta matuƙa, Wa zai san kanta?


“Ku juyo ku marasa aminci, Zan warkar da rashin amincinku. “To, ga shi, mun zo gare ka, Gama kai ne Ubangiji Allahnmu,


Ga shi, zan kawo wa birnin lafiya, gama zan warkar da su, in wadata su da salama da gaskiya.


Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu. Zan kuma ƙaunace su sosai, Gama fushina zai huce.


“Amma suka ƙi ji, suka ba da baya, suka toshe kunnuwansu don kada su ji.


Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.


don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”


ya ce, “Da ma a ce a yanzu kun san abubuwan da suke kawo salama. Amma ga shi, a yanzu a ɓoye suke a gare ku.


Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Wai don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’


Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,


Amma suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukar masa da nufi ɗaya,


Za su toshe kunnensu ga jin tatsuniyoyi.


Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.


ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar 'ya'ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al'ummai ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan