Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, zai kuwa samu a yalwace. Duk wanda kuma ba shi da shi, ko ɗan abin da yake da shi ma, za a karɓe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:12
17 Iomraidhean Croise  

“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.


Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.


To, me ubangijin garkan nan zai yi? Sai ya zo ya hallaka manoman nan, ya ba waɗansu garkar.


Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”


Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”


Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’


Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.


Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”


Duk wanda sai ya ji kunyar shaida ni da maganata, Ɗan Mutum ma zai ji kunyar shaida shi sa'ad da ya zo da ɗaukaka tasa, da kuma ɗaukakar Uba, da ta mala'iku tsarkaka.


Allah shi yake yin mayalwacin alheri. Domin haka Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali'u alheri.”


Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan