Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 13:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Ya amsa ya ce, “Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma su ba a ba su ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 13:11
40 Iomraidhean Croise  

Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.


Za a ɓoye muku ma'anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake.


Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.


Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake musu magana da misalai?”


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.


Amma ya ce musu, “Ba duk mutum ne zai iya ɗaukar maganar nan ba, sai dai waɗanda aka yardar wa.


Sai ya ce musu, “Lalle kwa sha ƙoƙona, amma zama a damana da haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda Ubana ya riga ya shirya wa ne.”


Amma zama a damana, ko a haguna, ba nawa ba ne da zan bayar, ai, na waɗanda aka riga aka shirya wa ne.”


Sai ya ce musu, “Ku kam, an yardar muku ku san asirin Mulkin Allah, amma ga waɗanda ba sa cikinku, kome sai a cikin misali,


Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.


Sai ya ƙara da cewa, “Shi ya sa na gaya muku, ba mai iya zuwa gare ni, sai ko Uba ya yardar masa.”


Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa.


Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.


'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.


Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal.


Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.


Ga shi, zan sanar da ku wani asiri! Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, amma dukanmu za a sauya kamanninmu,


Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.


Amma muna maganar asirtacciyar hikima ta Allah, wadda dā ɓoyayyiya ce, wato, hikimar da Allah ya ƙaddara tun gaban farkon zamanai, domin ɗaukakarmu.


Ta haka ya kamata a san mu da zama ma'aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al'amuran Allah.


Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?


a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,


ya sanasshe mu asirin nufinsa, bisa ga kyakkyawan nufinsa da ya nufa ya cika ta wurin Almasihu.


Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikkilisiya.


Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara,


Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta.


In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.


Ku kam, Mai Tsarkin nan ya shafe ku, dukanku kuma kun san gaskiya.


Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan