Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:46 - Littafi Mai Tsarki

46 Yana cikin magana da taro, sai ga Uwa tasa da 'yan'uwansa suna tsaye a waje, suna nema su yi magana da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

46 Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:46
26 Iomraidhean Croise  

Ga yadda haihuwar Yesu Almasihu take. Sa'ad da Yusufu yake tashin Maryamu mahaifiyar Yesu, tun ba a ɗauke ta ba, sai aka ga tana da juna biyu daga Ruhu Mai Tsarki.


Wani ya ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”


Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?


Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.


“Tashi ka ɗauki ɗan yaron da uwa tasa, ka tafi ƙasar Isra'ila, don masu neman ran ɗan yaron sun mutu.”


Ba mai mahon tsohuwar tufa da sabon ƙyalle. In ma an yi, ai, sai sabon ƙyallen ya kece tsohuwar tufar, har ma ta fi dā kecewa.


Shin, wannan ba shi ne masassaƙin nan ba, ɗan Maryamu, ɗan'uwan su Yakubu, da Yusufu, da Yahuza, da kuma Saminu? 'Yan'uwansa mata kuma ba ga su tare da mu ba?” Suka yi tuntuɓe sabili da shi.


Ta yaya wannan alheri ya same ni, har da uwar Ubangijina za ta zo gare ni?


Uwa tasa da ubansa kuwa suna mamakin abin da aka faɗa game da shi,


Sai Saminu ya sa musu albarka, ya ce wa Maryamu uwar Yesu, “Kin ga wannan yaro, shi aka sa ya zama sanadin faɗuwar waɗansu, tashin waɗansu kuma da yawa cikin Isra'ila, Zai kuma zama alama wadda ake kushenta,


Da suka gan shi suka yi mamaki, sai uwa tasa ta ce masa, “Ya kai ɗana, yaya ka yi mana haka? Ga shi nan, ni da babanka muna ta nemanka duk ranmu a ɓace.”


Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.


Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.


Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da uwa tasa, da 'yar'uwa tata, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye.


A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan,


Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.


Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.”


Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba.


Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi.


Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba.


Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.


Ba mu da ikon tafiya da matarmu ta aure mai bi, kamar yadda sauran manzanni, da 'yan'uwan Ubangiji, da kuma Kefas suke yi?


Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan'uwan Ubangiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan