Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:45 - Littafi Mai Tsarki

45 Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

45 Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:45
23 Iomraidhean Croise  

Firist zai dudduba shi, idan zurfin kumburin ko tabon rikiɗa fari, sai firist ya hurta, cewa, mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta ce ta faso a ƙurjin.


Amma da Farisiyawa suka ji haka sai suka ce, “Ai, da ikon Ba'alzabul sarkin aljannu kawai, wannan yake fitar da aljannu.”


Sa'an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa'ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce.


[Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a da azumi.]”


Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan kewaye ƙasashe da tekuna don samun almajiri ɗaya tak, in kuwa kun samu, kukan mai da shi ɗan wuta fiye da ku, ninkin ba ninkin.


Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!


[Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai.


Yesu ya tambaye shi, “Me sunanka?” Sai ya amsa ya ce, “Sunana Tuli, don muna da yawa.”


Daga nan sai ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum kuwa ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa.”


Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.


Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan