Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:44 - Littafi Mai Tsarki

44 Sa'an nan sai ya ce, ‘Zan koma gidana da na fito.’ Sa'ad da kuwa ya koma, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, ƙawatacce.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

44 Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:44
23 Iomraidhean Croise  

Zukatansu suna ƙuna da ƙullaƙulle kamar tanderu. Fushinsu na ci dare farai, Da safe fushinsu yana ci bal-bal kamar harshen wuta.


Yaya za a iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum a washe kayansa, in ba an fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin ba? Sa'an nan ne za a iya washe gidansa.


“Baƙin aljan in ya rabu da mutum, sai ya bi ta wurare marasa ruwa neman hutu, amma ba ya samu.


Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”


Sa'ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce,


Ya faɗi haka fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a'a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da yake ciki.


Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.


Da karɓar 'yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.”


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.


Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.


Ya ku 'ya'yana ƙanana, ku kam na Allah ne, kun kuma ci nasara a kan waɗannan, domin shi wanda yake zuciyarku ya fi wanda yake duniya ƙarfi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan