37 Maganarka ce za ta kuɓutar da kai, ko kuma ta hukunta ka.”
37 Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”
Ka lura da irin abin da kake faɗa don ka kiyaye ranka. Mutumin da bai kula da maganarsa ba, yakan hallakar da kansa.
Abin da ka faɗa ya iya cetonka ko ya hallaka ka, saboda haka tilas ne ka karɓi sakamakon maganarka.
Ina dai gaya muku, a Ranar Shari'a duk hululun da mutum ya yi, za a bincike shi.
Waɗansu malaman Attaura da Farisiyawa suka amsa masa suka ce, “Malam, muna so mu ga wata alama daga gare ka.”