Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Ku macizai! Yaya za ku iya yin maganar kirki, alhali kuwa ku mugaye ne? Don abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:34
28 Iomraidhean Croise  

Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah.” Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura, Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.


Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau.


Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu, Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu. “Ba wanda zai gan mu,” in ji su.


Mai hikima yakan yi tunani kafin ya yi magana, abin da ya faɗa yakan yi rinjaye ƙwarai.


Tunane-tunanenka mafarin rai ne kansa, ka kiyaye su abin mallakarka ne mafi daraja.


Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha.


Aikata gaskiya ya kawu, adalci ya tsaya daga can nesa, gama gaskiya ta fāɗi a dandali, sahihanci ba zai shiga ba.


Ba wanda yake kai ƙara ta gaskiya, ba wanda yake yanke shari'a da adalci. Kuna dogara ga shaidar ƙarya, kuna faɗar ƙarya, kuna ɗaukar ciki na ɓarna, ku haifi mugunta.


Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.


Mutumin kirki kam, ta kyakkyawar taskar zuciya tasa yakan yi abin kirki, mugu kuwa, ta mummunar taskar zuciya tasa yakan yi mugun abu.


Amma abin da ya fito ta baka, daga zuci yake, shi ne kuwa yake ƙazantar da mutum.


Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?


Amma da Yahaya ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa, sun taho domin a yi musu baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?


Saboda haka, Yahaya ya ce wa taron jama'ar da yake zuwa domin ya yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?


Mutumin kirki kam ta kyakkyawar taskar zuciyarsa yakan yi abin kirki, mugu kuwa ta mummunar taskar zuciyarsa yakan yi mugun abu. Ai, abin da ya ci rai, shi mutum yake faɗa.”


Ku na ubanku Iblis ne, niyyarku kuwa ku aikata burin ubanku. Shi dā ma tun farko mai kisankai ne, bai zauna kan gaskiya ba, don ba ruwansa da gaskiya. Duk sa'ad da yake ƙarya, cinikinsa yake yi, don shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.


Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.


Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.


Domin dukanmu muna yin kuskure da yawa. In kuwa mutum ba ya shirme a maganarsa, to, shi cikakken mutum ne, yana kuwa iya kame duk sauran gaɓoɓinsa ma.


Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.


Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan