Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:33 - Littafi Mai Tsarki

33 “Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 “Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:33
11 Iomraidhean Croise  

Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa'an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama'ar Isra'ila?


Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta, Ku yi adalci cikin majalisar alƙalanku! Watakila Ubangiji Allah Mai Runduna Zai yi wa sauran da suka ragu na wannan al'umma alheri.


Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.


Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”


Ya 'yan'uwana, ashe, ɓaure yana iya haifar zaitun? Ko kuwa inabi ya haifi ɓaure? Haka kuma, ba dama a sami ruwan daɗi a idon ruwan zartsi.


Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan