Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 12:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 12:32
35 Iomraidhean Croise  

“Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu, Suna tanada wa kansu fushi, Ba su neman taimako sa'ad da ya ɗaure su.


Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”


“Don haka ina gaya muku, ā gafarta wa mutane kowane zunubi da saɓo, amma wanda ya saɓi Ruhun, ba za a gafarta masa ba.


Domin Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabar.”


Wanda ya faɗa cikin ƙaya kuwa, shi ne wanda ya ji Maganar, amma taraddadin duniya da jarabar dukiya sukan sarƙe Maganar, har ta zama marar amfani.


Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne.


Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya.


Ashe, wannan ba ɗan masassaƙin nan ba ne? Uwa tasa ba sunanta Maryamu ba? 'Yan'uwansa kuwa ba su ne Yakubu, da Yusufu, da Saminu, da kuma Yahuza ba?


Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”


sa'an nan ya kasa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu, na gidaje, da 'yan'uwa mata, da 'yan'uwa maza, da iyaye mata, da 'ya'ya, da gonaki, amma game da tsanani, a lahira kuma ya sami rai madawwami.


“Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta,


amma fa, duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.”


Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.


Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.


sa'an nan ya kasa samun ninkinsu mai yawa a yanzu, a Lahira kuma ya sami rai madawwami.”


Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.


Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, kuna kuma cewa, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’


Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.”


To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.


Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”


Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,


a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.


ko da yake dā can sāɓo nake yi, ina tsanantarwa, ina wulakantarwa, duk da haka, sai dai aka yi mini jinƙai, domin na yi haka ne da jahilci saboda rashin bangaskiya.


Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.


Horon jiki yana da ɗan amfaninsa, amma bin Allah yana da amfani ta kowace hanya, da yake shi ne da alkawarin rai na a yanzu da na nan gaba.


Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.


domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.


yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah,


Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan